1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO za ta ci gaba da taimaka wa Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
October 3, 2024

Sakatare Janar na kungiyar NATO Mark Rutte ya kai ziyara Kyiv karon farko bayan da ya hau kan mukamin

https://p.dw.com/p/4lNZg
Ukraine | Shugaba Selenskyj  da sabon sakataren kungiyar NATO Mark Rutte
Hoto: Valentyn Ogirenko/REUTERS

Tsohon Firaministan Netherlands Mark Rutte ya isa Kyiv babban birnin Ukraine a ziyararsa ta farko bayan kama aiki a matsayin sabon shugaban kungiyar kawancen tsaro ta NATO.

Rutte ya gana da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a daidai lokacin da amsa kuwwa ya karade birnin Kyiv kan fargabar hari daga Rasha.

Sabon shugaban na NATO ya yi alkawarin cewa kasashen yamma za su cigaba da bai wa Ukraine goyon baya a yakin da ta ke yi na yantar da kanta daga hare haren Rasha.