1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO za ta binciki zargin kisan fararen hula a Libya

April 1, 2011

Sojojin NATO sun raunana ƙarfin dakarun Gaddafi yayin da fada ke cigaba da yin ƙamari a gabashin Libya

https://p.dw.com/p/10lgt
Sakatare janar na ƙungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh RasmussenHoto: dapd

Ƙungiyar ƙawance tsaro ta NATO ta ce tana gudanar da bincike akan rahoton da limaman Chochin Katolika na ƙasar Italiya suka gabatar a Tripoli cewa an kashe fararen hula aƙalla 40 a farmakin da aka kaiwa babban birnin ƙasar ta Libya. Sakatare janar na ƙungiyar tsaron ta NATO Anders Fogh Rasmussen yace suna bin ƙa'idar ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ya bada damar shiga tsakani domin kare rayuwar jama'a fararen hula " NATO za ta aiwatar da sashen nan na Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya wanda ya buƙaci kare rayuwar jama'a fararen hula". Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da NATO ta karɓi ragamar jagorancin matakin sojin akan Libya.

A waje guda kuma wani babban kwamandan sojin Amirka Admiral Mike Mullen yace farmakin haɗin gwiwa na dakarun NATO a Libya ya yi mummunan illa ga dakarun sojin Gaddafi, sai dai kuma yace har yanzu ba'a kai ga karya lagon sojojin baki ɗaya ba tukunna. A cigaba da gwabza ƙazamin fada tsakanin dakarun Gaddafi da yan tawaye a garin Brega mai arzikin mai dake gabashin Libyan, sojin 'yan tawaye sun ja da baya daga wasu yankunan da suka ƙwace bayan da dakarun sojin Gaddafi waɗanda suka ninkasu yawa suka riƙa yi musu luguden wuta.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Zainab Mohammed Abubakar