1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO: Ukraine na jinjinawa Stoltenberg

July 4, 2023

Gwamnatin Ukraine ta yi jinjina tare da taya murna wa Jens Stoltenberg bayan ba shi sabon wa'adi na shekara guda domin ci gaba da jagorantar kungiyar kawancen tsaro ta NATO.

https://p.dw.com/p/4TOzY
NATO | Abschluss der Air Defender Übung in Deutschland
Hoto: Christian Charisius/dpa/picture alliance

Mahukutan na Ukraine sun yaba da yadda Soltenberd dan asalin kasar Norwe ya tsaya wa kasar tsayin daka domin samun taffafin makamai da kuma horo wa sojojinta domin kara kanta daga mayamar da Rasha ta kaddamar mata yau da kusan shekara guda da rabi.

Yayin da yake tsokaci a shafinsa na Tweeter kan tsawaita wa'adin jagoranci wa shugaban kungiyar, ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kouleba ya wallafa cewar Jens Stoltemberg ya lankanci tafiyar da jagoranci cikin hikimar diflomasiyya sannan kuma Kiev na a shirye domin ci gaba da aiki tare da shi kafada da kafada a kokarin da take na samun galaba kan Rasha a yakin da suke fafatawa.