1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO za ta yi nazari kan fadan Siriya

Ramatu Garba Baba
October 24, 2019

Kungiyar NATO na shirin soma wani zama na musamman don tattaunawa kan babban taron da kungiyar za ta yi cikin watan Disamba mai zuwa, ana ganin taron zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a arewacin Siriya.

https://p.dw.com/p/3RpIG
Brüssel Nato-Hauptquartier
Hoto: Getty Images/AFP/M. Wenger

Yayin zaman na wannan Alhamis, ana sa ran ministan tsaron Turkiyya Hukudi Akar zai yi wa NATO din cikakken bayani kan halin da ake ciki kan fadan da kasarsa ke yi da Kurdawa a arewacin Siriya.Ita kuwa ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrebauer a nata bangaren za ta yi bayani ne dalla-dalla kan irin bukatar da ta rigaya ta mika ta samar da wani tudun na tsira a wajen da ake wannan dambarwa.

Gabannin wannan zama da za a yi dai, shugaban NATO din Jens Stoltenberg ya yaba da irin saukin da aka samu a fadan da ake yi bayan wata matsaya da aka cimma tsakanin Amirka da Turkiyya na tsagaita bude wuta. Fadan na baya-bayan nan ya tilasta ma daruruwa tserewa gidajensu da kuma tsaiko a gudanar da aikin agaji.