1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gargadi Rasha kan kera makaman kare dangi

Ramatu Garba Baba
February 12, 2019

Kungiyar NATO ta sake jan hankalin Rasha, kan ta dakatar da kera sabbin makamai masu linzami, maimakon hakan, ta dauki matakin warware takaddamar da ke a tsakaninta da Amirka bisa yarjejeniyar makaman masu hadari.

https://p.dw.com/p/3DDVk
NATO Jens Stoltenberg PK zum Ministertreffen in Brüssel
Hoto: picture-alliance/AA/D. Aydemir

Babban magatakardar na kungiyar tsaron, Jens Stoltenberg ne ya fadi hakan a wannan Talata, ya kara da cewa, kungiyar ta  NATO a shirye ta ke ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na kare yankin Turai amma duk da haka akwai bukatar a sassanta. Cikin watan Oktobar bara ne, Shugaba Donald Trump ya sanar da cewar kasar za ta yi watsi da yarjejeniyar makaman matukar Rasha ta ki bin umarnin kungiyar tsaron ta NATO kan sababbin makaman masu linzamin da ta kirkira.

A gobe Laraba ministoci a karkashin kungiyar za su yi wata ganawa ta kwanaki biyu a birnin Brussels don yin nazari kan sabbin matakan tsaro don kare yankin daga barnar da ake gudu makaman na Rasha ka iya haddasawa yankin Turan.