1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta jingine farmakin hadin gwiwa a Afghanistan

September 18, 2012

Kungiyar NATO ta sauya tunani dangane da farmakin hadin gwiwa da sojin Afghanistan.

https://p.dw.com/p/16BCf

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta sanar da takaita gudanar da farmakin hadin gwiwa da sojojin Afghanistan a matakin martani ga karuwar harin cikin gida akan dakarun ketare. Sai dai kuma ta ce wannan mataki ne na wucin gadi kuma ba zai shafi wa'din mika ragamar tsaro ga jami'an tsaron Afghanistan din a shekarar 2014 ba. Umarnin dakatarwar har illa ma sha Allahu na farmakin hadin gwiwa tsakanin sojojin NATO dana Afghanistan ya fito ne daga mukaddashin babban kwamandan sojin Amirka a Afghanistan Lt Janar James Terry kuma dokar ta shafi dukkan bataliyar soji wadda dakarunta basu wuce 800 ba. Sai dai kuma wani mai magana da yawun kungiyar NATO Kanar Tom Collins yace matakin lamari ne na wucin gadi.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman