1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta ji takaicin kuskuren kai hari akan 'yan tawayen Libya

April 8, 2011

NATO ta baiyana matuƙar damuwa da takaici game da kuskuren kai hari akan yan tawayen Libya

https://p.dw.com/p/10q8C
Hoto: AP

Ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO ta amince cewa ta yi kuskure a wani farmakin jiragen sama da ta kai a Libya wanda ya kuskure ya faɗa kan wani tanki na sojin yan tawaye a garin Brega. Mai magana da yawun NATO Russ Harding yace yanayin da ake fuskanta a ƙasa lamari ne mai sarƙaƙiya. A halin da ake ciki kuma ƙasar Turkiya na ƙoƙarin sasantawa tsakanin yan tawaye da magoya bayan Gaddafi. Firaministan Turkiyan Recep Tayyip Erdogan yace yana tattaunawa da ɓangarorin biyu zai kuma buƙaci bayar da damar kaiwa jama'a kayayyakin agajin da kuma share fagen aiwatar da garanbawul ta fuskar dimokraɗiyya. Sai dai kuma kakakin yan tawayen ya yi watsi da dukkan wata tattaunawa da Muammar Gaddafi yana mai cewa abinda suke buƙata shine ya sauka daga karagar mulki.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi