1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atasayin sojin NATO a Norway

Abdourahamane Hassane
March 14, 2022

An fara gudanar da gagarumin atisayin soji da ya kunshi sojoji dubu 30,000 na kungiyar tsaro ta NATO da kuma na kasashen da ke kawance da kungiyar a Norway.

https://p.dw.com/p/48SWY
Ukraine | Internationale Manöver „Rapid trident“ im Jahr 2019 in Yavoriw
Hoto: U.S. Army/Amanda H. Johnson

Atisayin wanda aka dade da tsarashi, na da manufar auna karfin kasar ta Norway na samun ƙarfafawa daga waje a yayin da wata ƙasa ta kaimata hari. Jiragen yaki sama da 200 da na ruwa kusan 50, ke cikin atisayin da za a kai har daya ga watan Afrilu ana yin sa, sai dai wani kakakin rundunar sojin Norway ya ce atisayen ba ya da alaka da yakin Ukraine. Kudirin da ke a ƙarƙashin sashe na biyar na yarjejeniyar NATO  shi ya wajabta mambobinta su ba da taimako ga ɗa yansu da ke fuskantar barazana.