1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO na shirin kara daukar mataki kan Rasha

Bernd Riegert, MAB
July 10, 2023

Kungiyar tsaro ta NATO na son tabbatar wa Ukraine kan za ta iya samun gurbi da zarar ta kammala yaki da take yi da Rasha. Ta ce za ta yi bayani a taronta na 11.07.2023

https://p.dw.com/p/4Tgjm
Hoto: Petras Malukas/AFP

A cikin shekaru 74 na tarihin kungiyar tsaro ta NATO, ba kasafai ne shugabannin gwamnatoci da shugabannin kasashe ke taro a kusa da kasar da suke gaba da ita ba. Hasali ma dai, Vilnius da ke zama babban birnin Lithuania, yana da nisan kilomita 200 kacal da iyakar Rasha da ke yankin Kaliningrad, yayin da Belarus da ke kawance da Rasha na da tazarar kilomita 35 daga Vilnius. Tabbas a shekara ta 2006, NATO ta yi taron kolinta a Riga na kasar Latvia, amma a lokacin tana daukar Rasha a matsayin abokiyar manufofin tsaro. kasar Lithuaniya da kawayenta na NATO sun tura sojoji kusan 4,000 don kare taron shugabannin kasashe da gwamnatoci mafi girma a tarihin kasar. Idan ma aka hada da 'yan sanda da jami'an sirri, kusan mutane 12,000 ne za su tabbatar da tsaro a ranaku biyu na taron na koli. Ita ma rundunar Bundeswehr ta Jamus ta bayar da gudunmawa, inda sojojinta na saman suke amfani da na'urorin Patriot don dakile yiwuwar harin makami mai linzami. Shugaban Lithuania Gitanas Nauseda ya ce kasarasa ta kashe Euro miliyan 38 a kan babban taron ciki har da fadada cibiyar baje koli ta Vilnius da ke daukar bakuncin taron kawancen soja. Gitanas Nauseda da ke goyon bayan burin Ukraine na shiga kungiyar tsaro na NATO na son kawancen ya nuna hadin kai game da wannan batu: "Wasu abokan aiki na cewa Putin mai karfi yana da karancin hadari fiye da Putin mai rauni. Amma ni ban yarda ba. Dole ne mu ci gaba da daukan matakai kuma mu yanke hukunci, saboda yanzu lokaci ne mai mahimmanci na tarihi. Idan ba mu yanke hukunci ba kuma ba mu hada kai a yanzu ba, muka bari gobe, za mu yi latti."

Sauran kasashen Turai na da ja a kan shigar Ukraine cikin NATO lokacin yaki

Litauen Vilnius | VOR dem NATO-Gipfel | Präsidentenpalast, Flaggen
Hoto: Petras Malukas/AFP/Getty Images

Shugaban Lithuania ya yi imanin cewa ya kamata a yi amfani da raunin da shugaban Rasha Vladimir Putin ke da shi a halin yanzu bayan boren sojojin haya na Wagner da bai yi nasara ba wajen aiwatar da ajenda NATO. Shi ma shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya bayyana burinsa a ziyarar da ya kai wasu kasashen kungiyar tsaro ta NATO a lokuta da dama da suka gabata, inda ya ce a shirye Ukraine take ta zama mamba a kungiyar Tsaro ta NATO: "Ukraine a shirye take ta kasance cikin kungiyar NATO. Muna jiran NATO ta ce a shirye take ta rungumi Ukraine a matsayin mamba. Ina ganin tabbacin tsaro yana da matukar muhimmanci ba ga Ukraine ka dai ba har ma da makwabtanmu kamar Moldova, saboda mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine na iya zama wata barazanar cin zarafi ga sauran sassan Turai." Amma shugaba gwamnatin Jamus Olaf Scholz, kamar wasu shugabannin gwamnatoci sun bayyana matsayinsu na rashin share wa ukraine hanyar samun kujera a kawancen tsaron a lokacin da take fama da yaki, yana mai cewa dokokin NATO sun tanadi zama memba ne ga kasashen da ba sa fama da rikicin kan iyakokinsu. Ya zuwa yanzu dai, ba a san tabbacin tsaro da manyan kasashen NATO ciki har da Amirka da Birtaniya da Faransa da Jamus za su yi ba wa Ukraine musamman bayan fatan kawo karshen yakin ba, lamarin da shi ma za a nemi warwarewa a taron na kasar Lithuania.