1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine za ta samu tallafin NATO

November 29, 2022

Ana sa ran taron na NATO ya yi tattaunawa ta gaggawa kan yadda za a taimaki Ukraine wajen samun makamashi mai dorewa bayan da Rasha ta kai wa cibiyoyin samar da lantarki hare-hare a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/4KFMv
Ministocin harkokin wajen kasashen NATO
Ministocin harkokin wajen kasashen NATOHoto: Daniel Mihailescu/AFP/Getty Images

Ministocin kula da harkokin ketare na kasashen da ke cikin kungiyar tsaro ta NATO, sun taru a birnin Bucharest na Romeniya a wannan Talata domin tattauna hanyoyin da za su ci gaba da tallafa wa Ukraine.

A jawabinsa na bude taron, Jens Stoltenberg, sakatare-janar na kungiyar ya ce NATO ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin fitar da Ukraine daga halin da take ciki. Stoltenberg ya ce babu gudu ba ja da baya, ministocin za su tabbatar Rasha ba ta yi nasara a kan Ukraine ba.

Tun kafin a fara wannan taro dai sakatare janar na NATO din ya yi zargin cewa Rasha na amfani da arzikin makamashi da take da shi a matsayin makami musamman a yanzu da aka shigo lokacin hunturu a Ukraine da kasashen Turai.