1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Islamisten gewinnen Ägypten-Wahl

January 23, 2012

Ƙungiyar 'yan uwa Musulmi da ta 'yan Salafiyya sun samu gagarumin rijnayen kujeru a majalisar dokokin Masar bayan sahihin zaɓe na farko da aka gudanar a ƙasar. A kan haka Rainer Sollich ya rubuta wannan sharhi

https://p.dw.com/p/13obM
Saad Al-Katatny (C), a Muslim Brotherhood's senior member, waves after being nominated by the Freedom and Justice Party for the post of the Parliament Speaker, during the first Egyptian parliament session after the revolution that ousted former President Hosni Mubarak, in Cairo January 23, 2012. Egypt's parliament began its first session on Monday since an election put Islamists in charge of the assembly following the overthrow of Mubarak in February. REUTERS/Khaled Elfiqi/Pool (EGYPT - Tags: POLITICS)
An buɗe zaman farko na sabuwar majalisar dokokin MasarHoto: Reuters

Hatta tsofon shugaban ƙasar Masar Hosni Mubarak yana tattare da masaniyar cewa idan har za a gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar to kuwa ba shakka masu kishin addinin musulunci ne zasu samu nasara. Da wannan hujjar ce hamɓararren shugaban ya ci gaba da mulki tsawon shekaru talatin tare da taimakon ƙasashen yammaci duk kuwa da take haƙƙin ɗan-Adam da yake yi. Ga alamu dai, bisa ga ra'ayin kasashen yammacin, kasancewar ƙasar ta Masar, wadda ta fi kowace yawan jama'a tsakanin ƙasashen Larabawa take kuma da muhimmanci ta fuskar tsaro, a ƙarkashin ikon masu tsananin kishin addini, ya fi muni akan mulki na danniya da kama karya da maguɗin zaɓe da azabtar da fursinoni, matsawar da za a ci gaba da samun daidaituwar manufofi na cikin gida da na ƙetare. Ala-kulli halin dai hasashen Mubarak gaskiya ne. Domin kuwa a sahihin zaɓe na farkon da aka gudanar a ƙasar ta Masar masu tsananin kishin addini ne suka lashe kashi saba'in cikin ɗari na kujeru a majalisar dokokin ƙasar. Domin kuwa a daura da ƙungiyar 'yan-uwa musulmi mai matsakaicin ra'ayi dake da kashi arba'in da biyar cikin ɗari, akwai ɗaya ƙungiyar ta Salafiyya mai zazzafan ra'ayin mazan-jiya, wadda aƙalla ta lashe kashi ɗaya bisa huɗu na jumullar ƙuri'un da aka kaɗa. Masu asarar zaɓen dai su ne jam'iyyu masu sassaucin ra'ayin siyasa da kuma ainihin matasa, waɗanda su ne suka jagoranci juyin-juya halin da ya kai ga murƙushe mulkin shugaba Hosni Mubarak.

Female members of parliament, who are also members of the Freedom and Justice Party of the Muslim Brotherhood, attend the first Egyptian parliament session after the revolution that ousted former President Hosni Mubarak, in Cairo January 23, 2012. Egypt's parliament began its first session on Monday since an election put Islamists in charge of the assembly following the overthrow of Mubarak in February. REUTERS/Khaled Elfiqi/Pool (EGYPT - Tags: POLITICS)
Wakilan sabuwar majalisar dokokin MasarHoto: Reuters

Sakamakon zaɓen dai ya bayyanar a fili cewar akasarin al'umar Masar, a halin da ake ciki yanzu, sun fi karkata ga jam'iyyun da ba su da wata nasaba da aƙidar demokraɗiyya da manufar daidaita sahu shigen na ƙasashen yammaci. Da yawa daga al'umar Masar sun fi sikankancewa ne da rawar da masu kishin addinin zasu taka wajen kyautata makomar jin daɗin rayuwarsu. To sai dai kuma da wuya hakan ta samu a cikin gaggawa ta la'akari da matsaloli na tattalin arziƙin da ƙasar ke fama da su, lamarin da ka iya sanya murna ta koma ciki. A baya ga haka su kansu sojojin ƙasar ba sa sha'awar sakin akalar mulkin dake hannunsu yanzu haka kuma akwai tababa a game da cewar zasu yarda su yi biyayya ga wata gwamnatin da aka naɗa a demokraɗiyyance. A saboda haka manazarta ke ganin ko dai a shiga gwagwarmayar kama madafun mulki tsakanin majalisar dokoki da soja ko kuma a raba madafun mulkin tsakanin janarorin sojan da 'yann uwa Musulmi. Amma fa kowace daga ɗayan hanyoyin biyu ta samu za a sake fuskantar adawa da ma tashe-tashen hankula a Masar. Dangane da ƙasashen Turai kuwa tilas ne su fara tattaunawa da 'yan-uwa musulmi kamar yadda lamarin ya kasance dangane da Amirka. Domin kuwa ƙungiyar ta ƙunshi ɓangarori daban-daban, kuma ƙungiyarb tarayyar Turai tana iya ba da goyan-baya ga ɓangarorin dake sha'awar demokraɗiyya da kamanta adalci, bisa manufa, tsakanin jama'a.

Mawallafi:Rainer Sollich/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani