1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rashin lafiyar Buhari ya dau hankalin PDP

Salissou Boukari
May 9, 2018

Babbar jam'iyar adawa ta PDP a Tarayyar Najeriya ta fitar da wata sanarwa, inda ta yi tsokaci kan yanayin lafiyar shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ya sake komawa asibiti a birnin London na Britaniya.

https://p.dw.com/p/2xRnv
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Jam'iyyar ta PDP ta ce hakan ya nunar cewa Shugaba Muhammdu Buhari ba zai iya tafiyar da jagorancin na Najeriya ba, inda ta ce ofishin na shugaban kasa a baya ya yi ta yi wa 'yan Najeriya karya kan halin rashin lafiyar ta Shugaban kasar, wanda har ya zuwa yanzu ba a san abun da ke damunsa ba. Shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari mai shekaru 75 da haihuwa, a baya ma dai ya shafe tsawon watanni sama da biyar yana zaman jinya a birnin London na Britaniya, sai dai kuma a rabnar Talata 08 ga watan nan na Mayu shugaban ya sake komawa asibitin, inda ake sa ran zai dawo a ran 12 ga wata.

Dama dai a makon da ya gabata shugaban na Najeriya ya sake tsawa a birnin na London bayan da ya fito daga wata ziyara a kasar Amirka inda ya gana da shugaban Amirka Donald Trump, amma dai fadar shugaban na Najeriya ta ce sake tsawar a birnin na London dalili ne na matsala daga jirgi, ba wai dan ganin likita ba.