1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka 'yan bindiga a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 3, 2022

Kimanin 'yan bindiga 200 ne jami'an tsaro suka halaka a jihar Niger da ke yankin Arewa maso Tsakiyar Najeriya, inda ake fama da matsalar rashin tsaro.

https://p.dw.com/p/47xwz
Najeriya I Matsalar 'Yan Bindiga
'Yan bindiga sun addabi al'umma a yankin Arewamaso Yammaci da Tsakiyar NajeriyaHoto: DW/Katrin Gänsler

Kwamishina mai kula da al'amuran tsaro na yankin Emmanuel Umar ne ya bayyana hakan, inda ya ce lamarin ya afku ne lokacin da jami'an tsaron ke kokarin kakkabe 'yan bindigar da suka addabi mutane da sacewa domin neman kudin fansa a wannan yankin. Ya kara da cewa daga cikin wadanda aka halaka har da wasu shugabannin 'yan bindigar, yna mai cewa sun kwace baburan 'yan ta'addan 60 da kuma wasu muggan makamai. Sai dai kuma kawo yanzu, kakakin rundunar sojojin kasar bai ce ufaffan ba kan batun.