1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari na son ya da kwallon mangoro

July 12, 2022

Kasa da watanni 10 da kai wa ya zuwa karshen wa'adin mulkinsa na shekaru takwas, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ce ya kagara ya sauka.

https://p.dw.com/p/4E2QA
Najeriya l Zaben Fidda da Gawni l Jam'iyyar APC
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Nigeria Prasidential Villa

Can a cikin Tarayyar Najeriya inda mafi yawan 'yan kasar ke kallon shugabanci da nufin inganta rayuwa dai, suna na shugaban kasar Muhammad Buhari na shan suka ko dai a kan batun rashin tsaro ko kuma kangi na talaucin da ke kara hadiye miliyoyin 'yan kasar a halin yanzu. Ana dai kallon gazawa a bangaren rashin tsaro, an kuma ce Buharin ya gaza a kokarin rage tsadar rayuwa ga al'umma ko bayan zarginsa da daure gindi ga barayin biron da ke yawo cikin kasar.

Duk da cewar dai a baya ya kasance mutum mafi farin jini a tsakanin masu siyasa ta kasar, sunan na Buhari yai nisa a cikin laka sakamakon matsalolin da Najeriyar ke fuskanta. Abun kuma da ga dukkan alamu ya kai wa shugaban iya wuya, sannan ya kai shi ga neman hanyar jefar da kwallon mangoro domin hutawa da kudan cikin kasar mai naci. Buharin dai ya ce ya kagara ya kammala wa'adin mulkin nasa, kuma ba shi da niyyar ya tsaya ko a Kaduna da ke zaman tsohuwar cibiyar rayuwa ta ritaya  har sai ya kai Daura da ke zaman mahaifar gado.