1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Bashi ya zama karfen kafa ga Najeriya

September 22, 2022

A yayin da mahukuntan Tarayyar Najeriya ke dada tsunduma cikin kogin bashi, suna kuma neman sake yafiya a karo na biyu cikin kasa da shekaru 20.

https://p.dw.com/p/4HERr
Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya | New York | Muhammadu Buhari | Najeriya
Shugaban Najeriya Muhhamdu BuhariHoto: Reuters/L. Jackson

Ko a farkon wannan mako dai mahukuntan Najeriyar sun tura wata bukatar cin bashin da ya kai Naira biliyan dubu 400 da miliyan biyu gaban majalisar dattawa ta kasar, a wani abun da ke nuna alamun nisan da kasar ta yi dangane da batun neman karatun bashin. Kama daga albashin ma'aikata ya zuwa manyan ayyuka da kokarin rage fatara dai, 'yan mukin Najeriyar sun koma zuwa dabarar cin bashin cikin yanayin da ke dada nuna alamun tsukewar lamura. Ya zuwa watan Satumbar da muke ciki dai bashin da ke wuyan kasar ya kai tiriliyan 43, yayin da ake saran zai karu zuwa tiriliyan 60 kafin mika mulki zuwa ga sabuwar gwamnati cikin watan Mayun badi.

Karin Bayani: Bashi na son zama karfen kafa ga Najeriya

To sai dai kuma daga dukkan alamu, mahukuntan Najeriyar sun kuma dauki sabuwar dabarar neman a yafe musu bashin da suke ta ci a halin yanzu. Can a birnin New York Na Amirka inda shugaban kasar Muhammadu Buhari ke halartar taron  babban zauren majalisar,  Buharin ya ce bashin na zaman tarnaki mai tsananin da yake bukatar a yafe shi ga daukacin kasashen da ke kokarin tashi. Kiran na shugaba Buhari dai na zaman na biyu cikin tsawon makonni biyu, domin ko a farkon watan nan na Satumba sai da mataimaki ga Buharin Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi a yafe bashin da nufin amfani da kudin wajen alkinta muhalli.

Najeriya | Tattalin Arziki | Daraja | Faduwa | Naira
Darajar Naira na kara faduwa, abin da ke kara janyo illa ga tattalin arzikin NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

To sai dai kuma kara daga murya cikin sunan bashin da a fadar Farfesa Mutakka Muhammad Usman da ke zaman kwararre kan tattalin arziki, zai wahala yayi tasirin da masu mulkin kasar ke fatan su gani. Kokarin mai da kai wajen mulkin al'umma ko kuma 'yar murya da nufin cika buri dai, Najeriyar ta ci moriyar yafiyar wani bashin da ya kai dalar Amirka miliyan dubu 12 shekaru 26 da suka gabata. To sai dai kuma, an kare tare da sake tara sabon bashin da yake rinjayar 'yan mulkin cikin kasar a halin yanzu. Raguwar yawan man da kasar ke haka gami da dimbin manyan ayyukan da ke gaban mahukuntan dai, ya saka bashin kai wa iya wuya ga Abujar.

Karin Bayani: Shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya

Sama da kaso 53 cikin 100 na kudin shigar Najeriyar dai, na tafiya ne ga biyan bashin manyan hukumomin kudi na duniya. Kuma a tunanin Yusha'u Aliyu da ke sharhi ga batun tattalin arzikin Najeriyar, kira na neman a yafe bashin na zaman siyasa ta duniya mai tasiri. Koma ta ina 'yan mulkin ke fatan bi da zumar nema na sa'idar bashin dai, ya zuwa yanzu bashin da ake bin hukumomi na zaman barazana mai girma a idanun shugabannin da ke dada tsoron tunkarar talakawa da batun karin haraji. Duk da yawan al'umma da ma girma na tattalin arzikin da babu kamarsa a nahiyar Afirka dai, batun biyan haraji na zama bako a tsakanin sarakuna da ma talakawan kasar.