1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miyanmar: An jibge tankokin yaki

February 16, 2021

Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi sojoji a Miyanmar dasu mutunta yancin bil adama ko kuma su fuskanci fushinta.

https://p.dw.com/p/3pPYE
Myanmar | Proteste nach Militärputsch
Hoto: AP/dpa/picture alliance

Bayan jibge tankokin yaki a wasu manyan titunan kasar Myanmar, Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa sojojin juyin mulki a kasar albishir da mummunan mataki, saboda amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin.

An samu raguwar masu zanga-zangar a jiya Litinin sakamakon motocin yakin da aka gani a manyan biranen kasar da aka yi wa damakaradiya karan tsaye.

Wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya, Farhan Haq, ya tabbatar da wata ganawa da aka yi jiya a tsakanin wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a Myanmar da mataimakin jagoran 'yan juyin mulkin, inda ta bukace su da mutunta 'yancin dan Adam kuma ta gargade su da su kauce wa sake tsinke hanyoyin sadarwa.