1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar sojin SADC ta haifar da muhawara a Kwango

Suleiman Babayo
April 10, 2024

Mutuwar sojin Tanzaniya ta sanya ayar tambaya a game da tasirin rundunar kiyaye zaman lafiya ta SADC na iya murkushe yan kungiyar M23 a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

https://p.dw.com/p/4edJe
Demokratische Republik Kongo |  Militärgouverneur der Provinz Nord-Kivu Peter Chirimwami
Hoto: picture alliance / Xinhua News Agency

Hallaka dakarun kiyaye zaman lafiya uku 'yan kasar Tanzaniya a rikicin da ke faruwa na yankin gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango ya haifar da zazzafar muhawara game da rikicin

Dakarun uku na kasar Tanzaniya da ke cikin rundunar kiyaye zaman lafiya na kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen kudancin Afirka SADC sun halaka ne lokacin da aka kai musu hari da makamin roka, lamarin da ya haifar da tambayoyi game da karfin dakarun na iya kakkabe mayakan tawaye na kungiyar M23, masu tayar da hankali a gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango. Dakarun sun fito daga kasashen Afirka ta Kudu, da Malawi da Tanzaniya, inda suka fara aiki a watan Disamba bayan kasashe 16 mambobin kungiyar sun amince da haka. Ita ma kasar Afirka ta Kudu an halaka mata sojoji biyu cikin watan Febrairu a wannan sansani.

Yankin Minova a Jamhuriyar dimukuradiyyar Congo
Yankin Minova a Jamhuriyar dimukuradiyyar CongoHoto: ALEXIS HUGUET/AFP

Gilbert Khadiagala masanin siyasar kasa da kasa ne.

"Yanzu rahotannin game da Tanzaniya abin tashin hankali ne. Me haka ya shaida mun, shi ne kungiyar M23 tana shirye da ta mayar da martani.

Ita dai kungiyar M23 wadda cikin shekara ta 2021 ta sake farfadowa ta kwace yankuna da dama cikin Lardin Kivu, inda ta kuma dumfari birnin Goma fadar gwamnatin lardin. Tuni lamarin ya haifar da tabarbarewar harkokin jinkai a yankin na gabashin Jamhuriyar Dimukadiyyar Kwango.

Sannan Gilbert Khadiagala masanin siyasar kasa da kasa ya kara da cewa:

"Ina ganin za a samu karin dakarun da za su mutu saboda yankin yana da matukar girma kuma sabon wuri ne ga dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar SADC. Ina tunanin yana da matukar wuya ga baki, wannan shi ne ya sa kungiyar M23 take da wata dama, ga kuma magoya baya. Sun san yankin abin da ya sa suka shiga gaban dakarun kungiyar SADC.

Fargabar yan tawaye a Gabashin Kwango
Fargabar yan tawaye a Gabashin Kwango Hoto: AUBIN MUKONI/AFP

Ana zargin kasar Ruwanda da ba da goyon baya ga 'yan tawayen na M23 musamman na makamai na zamani.

Stephanie Wolters babbar mai bincike kan kasashen yankin da ke cibiyar nazarain harkokin kasa da kasa ta Afirka ta Kudu tana ganin ya dace a nemi magance rikicin ta hanyar zama teburin sulhu maimako amfani da karfi kadai:

"Muna magana ce kan yanayi mafi dacewa inda kungiyar SADC ta yi amfani da kwarewa na soja domin sanya matsin lamba kan kungiyar M23 da haka zai tilasta Ruwanda hawa teburin da mika wuya kan goyon bayan kungiyar M23."

Dakarun na kungiyar kasashen SADC sun fara isa kasar ta Jamhuriyar Dimukaraidyyar Kwango lokacin da aka fara janye dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dubu-15. Kawo yanzu dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar SADC ba su taka kara sun karya ba duba da irin yawan sojojin da ake bukata domin dakile rikicin.