1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar mutane 150 a rikicn tawayen Sudan

February 28, 2012

Faɗa tsakanin 'yan tawaye da kuma sojojin gwamnatin Suudan na ci gaba da salwantar da rayukan mutane da dama akan iyakar ƙasar da Sudan ta kudu.

https://p.dw.com/p/14BSB
Soldaten der Rebellenorganisation «Sudanesische Befreiungsarmee» (SLA) patrouillieren in Muhujariya in Süden der sudanesischen Provinz Darfur (Archivfoto vom 25.04.2005). In der westsudanesischen Region Darfur spielt sich seit 2003 eine Tragödie ab. In dem Konflikt zwischen den rebellierenden Stämmen und der Zentralregierung starben bislang nach Angaben des Auswärtigen Amtes schätzungsweise 300 000 Menschen, über zwei Millionen Menschen mussten fliehen. Ein Friedensabkommen zwischen Khartum und der Rebellenorganisation «Sudanesische Befreiungsarmee» (SLA) vom Mai 2006 wurde bereits einen Monat später von den Aufständischen wieder annulliert. Jetzt hat Verteidigungsminister Jung (CDU) erklärt, Deutschland könnte im Rahmen eines UN-Mandats deutsche Soldaten auch nach Darfur entsenden. EPA/khaled el Fiqi (zu dpa 4462) +++(c) dpa - Bildfunk+++
'Yan tawayen Darfur na daga cikin masu yakar gwamnatin Sudan.Hoto: picture alliance/dpa

'Yan tawayen sudan sun bayyana cewar sun kashe dakarun gwamnati 150 a lokacin wani fito na fito da ya gudana tsakaninsu akan iyakar ƙasarsu da sudan ta kudu. Sai dai fadar mulki ta Khartoum ta ce akwai ƙarin gishiri a cikin labarin, ta na mai bayyana cewar sojojinta ne suka yi nasarar halaka 'yan tawaye da ta ce suna samun ɗaurin gindi da makobciyar ƙasa wato sudan ta kudu.

Ƙungiyar 'yan tawaye ta SPLM ta bayyana cewa tun a ranar lahadi ne ta kai harin haɗin guywa da takwararta ta Jem a Jau, wato wani yanki mai arzikin man fetur da kan iyaka. wannan dai shi ne karon farko da ƙungiyoyin 'yan tawayen biyu suka haɗa karfi domin yaƙar gwamnatin sudan. Sai dai hukumomin khartum suka ce sojojin kudancin sudan ne suka taimaka wa 'yan tawayen afka musu da faɗa. Lamarin a cewarsu ya saɓawa yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da aka cimma makwani biyun da suka gabata tsakanin sudan da kuma sudan ta kudu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu