Mutuwar karin mutane a Siriya
November 10, 2011Aƙalla mutane 12 suka rasa rayukansu a ƙasar Siriya a cigaba da farmakin da sojoji ke kaiwa masu zanga-zangar neman sauyi. Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama da suka bada wannan labari sun ce wadanda suka muntun sun haɗa da wata 'yar ƙaramar yarinya guda da kuma sojoji shidda.
A ɗaya hannun ƙungiyoyin ƙwadago sun shiga yajin aikin gama gari a yankin Jabal al-Zaouiya domin nuna adawa ga matakain da gwamnatin ke ɗauka kan masu zanga-zanga.
A halin da ake ciki kuma, komitin da 'yan adawa suka girka na cigaba da rangadi a ƙasashen yankin Golf domin samun goyan baya ga buƙatarsu ta gurfanar da hukumomin Siriya gaban kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta manyan lafukan yaƙi.
Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewar daga farkon rikicin Siriya zuwa yanzu fiye da mutane 3.500 su ka rasa rayukansu.
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Usman Shehu Usman