1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin da mutuwar al-Baghdadi zai yi cikin IS

Mohammad Nasiru Awal
October 31, 2019

A wani farmaki da dakarun Amirka na musamman suka kai cikin wani yanki na kasar Siriya, sun halaka jagoran kungiyar 'yan ta'adda ta IS, Abu Bakr al-Baghdadi.

https://p.dw.com/p/3SHF6
Abu Bakr al-Bagdadi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/

Shugaba Donald Trump na Amirka ya bayar da umurnin kai farmakin da kashe jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi dan shekaru 48 da haihuwa haifaffen kasar Iraki. Shugaban na Amirka ya yaba da hadin kai da ya samu daga sauran kasashen da ke da ruwa da tsaki a rikicin Siriya.