1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mutum tara sun rasu a wani hari kan asibitin Sudan

December 14, 2024

Harin da aka kaddamar kan asibitin na birnin Al-Fashir ya halaka marasa lafiya da kuma masu yi musu jinya.

https://p.dw.com/p/4o9kV
Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan da Mohamed Hamdan Dagalo
Hoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Wani hari da aka kaddamar kan asibiti a birnin Al-Fashir da ke yammacin Sudan ya halaka mutane tara, tare da raunata 20 ciki har da marasa lafiya da iyalansu a cewar shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce hare-hare kan asibitoci a Sudan sun zama ruwan dare.

Sojojin Sudan sun yi harbi a asibiti

Ya kuma yi kira da a rika kare dukkan marasa lafiya da ma'aikatan kiwon lafiya, da kuma dukkan wuraren jinya.

Tun a watan Afrilun 2023 ne yaki ya fara yayyaga Sudan, inda ake ta fafatawa tsakanin janar-janar guda biyu wato shugaban sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci daukar matakin gaggawa kan yakin Sudan

Tun a watan Mayun wannan shekaran ne Al-Fashir da ya kasance babban birnin Arewacin yankin Darfur, ya fada karkashin sojojin kar-ta-kwana na RSF wadanda suka toshe cinikayya da kuma kayan agaji a yankin.