1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari a sansanin 'yan gudun hijira

Abdul-raheem Hassan
March 20, 2022

Kungiyar agaji ta Red Cross ta tabbatar da mutuwar fararen hula 14 ciki har da kananan yara bakwai, a wani harin da 'yan tawaye suka kai a sansanin 'yan gudun hijira da ke arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/48klx

Wani shugaban al'umma a yankin Djugu da ke Ituri, ya ce wadan da suka kai harin 'yan wata fitacciyar kungiya ce mai dauke da makami mai suna CODECO, wadanda ake zargi da kisan kiyashi da kabilanci a yankin.

CODECO kungiya ce mai ra'ayin siyasa da addini wacce ke ikirarin wakiltar muradun kabilar Lendu a JDK, wasu rahotanni na cewa a yankin Beni da ke makwabtaka, an kashe matasa hudu a wani harin kwantan bauna da 'yan tawayen ADF suka kai a yau Lahadi a wani kauye mai nisan kilomita uku kacal daga Eringeti a cewar jami'in gwamnan lardin Kivu ta Arewa.