1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a gundumar Deir Essor a Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 13, 2018

Rahotanni daga kasar Siriya na nuni da cewa adadin fararen hular da suka hallaka yayin wani hari ta sama a gabashin gundumar Deir Essor, ya kai sama da 50.

https://p.dw.com/p/31QbT
Syrien Kämpfe in Deir Essor
Hari ta sama a gundumar Deir EssorHoto: Imago/Zuma Press

Masu rajin kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya da kuma kamfanin dillancin labaran kasar ta Siriya Sana, sun ruwaito cewa harin ya faru ne a kusa da kauyen Sussa da ke yankin gabashin gundumar ta Deir Essor, da ke karkashin ikon 'yan ta'addan IS. Mahukuntan na Siriya dai sun ruwaito cewa kimanin mutane 30 ne suka hallaka yayin harin da kawo yanzu ba a kai ga sanin wanda ya kai shi ba.