Ana ci gaba da tserewa kudancin Siriya
July 2, 2018Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane dubu 160 ne suka bar muhallansu cikin makonni biyu bayan fara kaddamar da hare-haren kwace iko da kudancin kasar daga hannun 'yan tawaye, mutanen na samun mafaka a yankunan da ke kusa da iyakar Isra'aila da Jordan, sai dai Isra'ila ta killace kan iyakarta.
A yanzu dai MDD na nuna fargabar tsananin mawuyacin hali da jama'a za su shiga sakamakon rashin shiga da kayan agaji yankunan da ake kai hare-haren, amma ministan harkokin wajen Jordan Ayman al-Safadi ya ce zai tattauna batun tsagaita wuta a ziyarar da zai kai kasar Rasha domin ba wa kungiyoyin agaji damar kai agaji ga dubban fararen hula.