Barazanar karancin abinci ga jama'a a yammacin Afirka
April 21, 2020Talla
Annboar coronavirus da matsalar fari da tabarbarewar tsaro da ke ci gaba addabar yankin Afirka ta Yamma na haddasa barazanar yunwa ga mutun miliyan 50 kamar yadda wani bincike da kungiyar agaji Oxfam ta bayyana.
Kungiyar ta ce za a samu adadin ne a cikin watan Augusta inda zai zarta na mutun miliyan 17 da aka yi hasashe kyautata zaton za su fuskanci karancin abinci a cikin watan Yuni.
Binciken ya ce duk da matakan da gwamnatocin kasashen da ke yammacin Afirka ke ci gaba da dauka, al'ummomin kasashen musamman ma a karkara na fama da matsaloli na samun kayayakin abinci bisa matakan dokokin kulle da hukumomi ke dauka da rufe iyakokin kasashen baya ga rashin tabbatacen tsaro da wasu kasashen ke fama da shi inji kungiyar.