1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane fiye da 200 sun mutu a Siriya

February 4, 2012

Yayin da kwamitin sulhu ke shirin kaɗa ƙuri'ar Allah wadai akan Siriya, rahotanni sun ce an kashe mutane fiye da 200 a birnin Homs.

https://p.dw.com/p/13ww9
Demonstrators take part in a protest against Syria's President Bashar al-Assad after Friday prayers in Baba Amro, near Homs February 3, 2012. REUTERS/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Dubban 'yan zanga zangar adawa da gwamnantin Assad na SiriyaHoto: REUTERS

Wakilan kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin kaɗa ƙuri'a a yau Asabar domin zartar da ƙudirin yin Allah wadai da matakin ƙarfi da Siriya ke ɗauka akan masu zanga zangar ƙin jinin gwamnatin. Jakadan Birtaniya a Majalisar Ɗinkin Duniya Mark Lyall Grant yace dukkan wakilai za su nemi umarnin ƙasashensu gabanin kaɗa ƙuri'ar

A waje guda kuma wata ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama wadda ke da mazauninta a Birtaniya ta ce jami'an tsaron Siriya sun kashe mutane fiye da 200 fararen hula waɗanda suka haɗa da mata da ƙananan yara a birnin Homs. Ƙungiyar ta sa ido kan haƙƙin bil Adama a Siriya ta ce daga cikin adadin, mutane 138 sun rasa rayukansu ne sakamakon buɗe musu wuta da tankokin yaƙi yayin da wasu mutanen 79 kuma an kashe su ne a wasu sassan birnin na Homs.

Ƙungiyar rajin kare haƙƙin al'umar Siriyan ta ce tarzomar ta ɓarke ne bayan da dubban jama'a a faɗin Siriya suka yi watsi da dirar mikiyar gwamnati suka fita domin tunawa da cikar shekaru 30 da mummunan kisan gillar da aka yiwa dubban jama'a mazauna garin Hama a shekarar 1982.

Babu dai tabbas ko ƙasar Rasha za ta bada goyon baya ga daftarin ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniyar. Tun da farko ta yi watsi da daftarin ƙudirin wanda ya buƙaci shugaban Siriya Bashar al-Assad ya sauka daga karagar mulki.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi