1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun mutu a fashewar wasu abubuwa a Kaduna

December 7, 2011

Bayanai masu karo da juna sun ce harin bam aka kai, yayin da wasu kafofin suka ce hatsari ne ya auku a wani shagon sayar da tukanen gas.

https://p.dw.com/p/13OJ4
Kaduna na fama da rikice rikice iri dabam dabamHoto: DW

Rahotanni daga garin Kaduna dake arewacin Najeriya sun nuna cewa aƙalla mutane shida sun rasu sannan wasu sun jikata a fashewar wasu abubuwa. Mazauna garin da kuma 'yan sanda sun ce bisa ga dukkan alamu hatsari ne amma ba harin bam aka kai ba. Kakakin 'yan sanda Aminu Lawan ya ce da farko sun yi zaton tashin bam ne amma binciken farko ya nuna cewa hatsari ne a wani shago dake sayar da baturan mota da tukane gas. To sai dai wasu rahotannin sun ce mutane 10 ne suka rasu ciki har da wata mace mai juna biyu da kananan yara biyu. Shaidun ganin ido sun fadawa manema labarai cewa sun ga baƙin hayaƙi ya tirnike wani yanki mai girma. Wannan dai ya zo ne kwana guda bayan kammala wani babban taron kwanaki biyu a garin na Kaduna da nufin wanzar da zaman lafiya ta hanyar shawarwari tsakanin shugabannin yanki da 'ya'yan ƙungiyar Boko Haram. A gun taron dai an yi kira da ƙirƙiro guraben aiki a wani mataki na rage zaman ɗarɗar da yawan rashin aikin ke haddasawa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu