1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Bukatar daina barin wuta

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 11, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci mahukuntan Habasha su gaggauta dakatar da yin barin wuta da jiragen yaki.

https://p.dw.com/p/45Mql
Antonio Guterres yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio GuterresHoto: Eduardo Munoz/REUTERS

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ne ya bukaci da gaggauta tsagaita wutar, sakamkon wani rahoto da ya bayyana kisan fararen hula sama da 50. Guterres ya bayyana takaicinsa dangane kisan fararen hular da ake ci gaba da samu, wanda kuma aka dora alhakinsa a kan barin wutar da jiragen yakin gwamnati suka yi a yankin a rewacin kasar.