1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Mutane 41 sun mutu a Turkiyya

Suleiman Babayo USU
October 15, 2022

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya ba da umurnin bincike yayin da aka fara zana'idar mutane 41 da suka mutu sakamakon fashewa a wajen hakar ma'adanai na arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4IF83
Turkiyya | Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya lokacin ziyarar inda aka samu hadari wajen hakar ma'adanai
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na TurkiyyaHoto: Press Office of the Presidency of Turkey/AFP

An fara zana'idar masu hakar ma'adanai na arewacin kasar Turkiyya sakamakon wata fashewa da aka samu inda mutane 41 suka halaka. 'Yan uwa da abokan arziki na masu hakar ma'adanan sun kwashe tsawon dare zuwa wayewar garin wannan Asabar domin samun labarin ma'aikatan a garin Amasra da aka samu fashewar lokacin da mutanen suke aiki a karkashin kasa.

Akwai kimanin masu hakar ma'adanai 110 lokacin da aka samu wannan fashewa. Masu aikin ceto suka iya fito da matanen da hadarin ya ritsa da su.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya kai ziyara inda aka samu hadarin aka kuma tantance mutane 41 sun mutu.