1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Mutane 179 sun mutu a hadarin jirgi a Koriya ta Kudu

December 29, 2024

Hukumomi a Koriya ta Kudu na ci gaba da bincike kan musabbabin hadarin jirgin saman fasinja mai dauke da mutane 181, gabanin ya sauka a filin jiragen sama na Muan da ke Koriya daga birnin Bangkok na kasar Thailand.

https://p.dw.com/p/4oehK
Jirgin saman kamfanin Jeju mai dauke da mutane 181 a lokacin da ya yi hadari a Koriya ta Kudu
Jirgin saman kamfanin Jeju mai dauke da mutane 181 a lokacin da ya yi hadari a Koriya ta KuduHoto: Yonhap via REUTERS

Ministan Sufuri na Koriya ta Kudu ya ce kamanin mutane  179 suka mutu kamar yadda jami'an hukumar kashe gobara suka bayyana duk da cewa adadin ka iya zarta hakan. Kafofin yada labaran kasar sun ce jirgin ya fuskanci matsalar birki gabanin ya kammala sauka wanda daga bisani ya daki katangar wani gini inda jirgin ya kama da wuta.

Karin bayani: Jirgin sama ya kama da wuta bayan hadari a Tokyo na Japan

Wannan ne karon farko da jirgin na kamfanin Jeju Air ya yi hadari tun bayan assasa kamfanin a shekara ta 2005, wanda kuma ke jigilar matsakaitan fasinjoji.

Hadarin jirgin na zuwa ne kwanaki da wani makamancinsa da ya faru da wani jirgin saman Azerbaijan, da ya janyo asarar rayuka.