1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Museveni na son mulkin mutu ka raba

Yusuf Bala Nayaya
July 27, 2018

Lauya da ke kare shugabannin 'yan adawa a Yuganda ya yi gargadin cewa Shugaba Yoweri Museveni dan shekaru 73 ya tasamma mulkin "mutu ka raba" bayan da kotu ta jaddada amincewa da kawar da batun shekaru ga shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/32CaI
Yoweri Museveni | Gericht in Uganda ermöglicht Langzeit-Präsident Museveni weitere Amtszeiten
Hoto: picture alliance/AP Photo/B. Chol

A baya dai doka ta tsara cewa shugaban kasa ya zama wajibi ya kasance yana kasa da shekaru 75, wannan kuwa da zai iya zama karan tsaye ga Museveni da ke kan mulki tun a 1986, ya nemi a sake zabensa a shekarar 2021.

'Yan adawa dai a Yuganda sun yi fatali da shirin majalisar dokokin kasar a watan Disamba bayan da suka amince da cire ka'idar shekarun ga shugaban kasa, lamarin da ya haifar da zanga-zanga har da garzayawarsu kotu don kalubalantar matakin da a yanzu kotun ta sake jaddadawa.