1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Museveni ya samu wa'adi na shida na mulki

Binta Aliyu Zurmi MAB
January 16, 2021

Hukumar zaben kasar Yuganda ta sanar da shugaba mai ci yanzu Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana a kasar a wannan Alhamis din da ta gabata, inda ya fafata da 'yan takara goma.

https://p.dw.com/p/3o1Qj
Großbritannien London 2020 | Yoweri Museveni, Präsident Uganda
Hoto: Henry Nicholls/REUTERS

Shugaba Museveni da ya kwashe tsawon shekaru 35 yana jan ragamar mulkin kasar zai kara wani sabon wa'adi na shidda, kuma yana daga cikin shugabannin Afirka da suka fi dadewa a kan mulki. Museveni ya samu kashi 58,6% a gaban matashin dan adawa mai shekaru 48 a duniya Bobi Wine, wanda  ya tashi da kashi 34,8% na kuri'un da aka kada.

A yayin sanar da wannan sakamakon zaben madugun adawa ya sanar da cewar jami'an tsaro sun kewayen gidansa, lamarin da ya ce ya sanya rayuwarsa cikin wani babban hadari. sai dai kuma a nata bangaren gwamnati ta ce tana bashi kariya ne. Tun kafin a kai ga fidda sakamakon karshe Bobi Wine ya yi watsi da sakamakon saboda a cewarsa an yi aringizon kuri'u.