1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin sulhunta Armeniya da Azerbaijan

October 10, 2022

Kasashen Armeniya da Azerbaijan za su yi musayar fursunoni kimanin 17 a matakin farko na son ganin sun shawo kan rigingimun da suka hanasu zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/4I0pZ
Yankin Nagorno-Karabakh Hoto: ARIS MESSINIS/AFP

Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ne ya shiga tsakani don ganin an yi sulhu a tsakanin Armeniya da makwabciyarta Azerbaijan da suka jima suna fada da juna, a matakin farko da ke nuna an kama hanyar sulhunta rikicin, bangarorin biyu sun amince su yi musayar fursunoni kimanin goma sha bakwai, an cimma matsayar bayan wata tattaunawa da Mista Blinken ya yi ta wayar tarho da Shugaba Ilham Aliyev na Azerbaijan a wannan Litinin.

Blinken ya kuma bayyana aniyar Amirka na ba su goyon baya wurin warware muhimman batutuwan da suka haifar da sabanin, musamman bayar da damar hawa teburin sulhu kan yankin nan na Nagorno-Karabakh da suka jima suna jayayya a kai. Rayuka fiye da dari biyu ne suka salwanta a rikicin baya-bayan nan a tsakanin makwabtan biyu.