1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Mun karbe ikon gudanar da shari'ar zabe daga kotuna'

September 28, 2024

Majalisar dokokin Tunisiya ta ragewa bangaren shari'a karfi tare kuma da karbe ikon gudanar da hukuncin karshe kan al'amuran da suka shafi zabe. Matakin da 'yan adawa ke kallon zai bawa shugaba Kais Saied damar tazarce.

https://p.dw.com/p/4lBjh
Shugaba Kais Saied na kasar Tunisiya
Shugaba Kais Saied na kasar TunisiyaHoto: Chokri Mahjoub/ZUMA Wire/IMAGO

Matakin 'yan majalisar na zuwa ne gabanin babban zaben shugaban kasar da za a gudanar a kasa da kwanaki 10. 'Yan majalisa 116 daga cikin 161 ne suka kada kuri'ar ragewa bangaren shari'a ikon yanke hukunci kan zabe.

ME AL'UMMA YA KAMATA SU SANI GAME DA DOKAR?

Dokar dai ta dakatar da alkalan kotun kundin tsarin mulkin kasar daga gudanar da shari'un da suka shafi zabe, baya ga korar alkalan kotun kolin kasar da shugaba Kais Saied ya yi a shekara ta 2022, bayan takun sakar da ke tsakanin bangaren shari'ar da kuma hukumar zaben kasar, wanda shugaba Saied ne ya nada mambobinta.

Karin bayani: Fushin matasa na kara tsananta gabanin zabe a Tunisiya 

Tun dai 'yan adawa da kungiyoyin farar hula suka kira gangamin nuna adawa da matakin 'yan majalisar dokokin kasar.