1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mulkin kan yankin Kudancin Sudan

July 8, 2011

Tabbatarwa da yankin kudancin sudan 'yancin cin gashin kai a ranar Asabar 9 ga watan Yuli, na nufin cikawa al'ummomin wannan yanki na Sudan mafarkinsu na tsawon shekaru 50 tare da kawo karshen yaki da zub da jini.

https://p.dw.com/p/11rgk
Murnar mulkin kai a kudancin SudanHoto: picture alliance/dpa

Kusan mutane miliyan biyu ne dai suka rasa rayukansu, a yayinda wasu miliyan huɗu suka rasa matsugunnensu. Yaƙin da ya fara tun kafin samun 'yancin kan Sudan ɗin a shekara ta 1955, wanda ya kunshi batutuwa da dama a tarihin wannan ƙasa. Zainab Mohammad Abubakar na dauke da karin bayani.....
Taken yankin kudancin sudan kenan, wanda a sama da shekaru 50 da suka gaabata babu wanda ya taɓa tunanin cewar ranar rerata zata zo. A shekaaara ta 1955 nedai Sudan ta samu 'yancin kai daga mulkin mallaka, sai dai baza'a iya cewar iyakokin kasar sun tsira daga mulkin mallaka ba. Domin har ya zuwa karni na goma sha tara 'yan kasuwar yankin arewacin Sudan sukan sace mutane daga kudancin. Lamarin ba daban yake ba tun zamanin da kasar take karkashin mulkin mallaka.

Gidan Radiyo dai wata kafa ce ta sadarwa tsakanin ɓangarorin. Amma sojojin kungiyar SPLA na adawa da yankin arewacin kasar.Sojojinsu na kai hari sojojin arewacin kasar, tare da amfani da jiragen sama, da kwace birane. Sai dai muradun mayakan na SPLA bai fito fili ba a wancan lokaci.

"Muna yaƙi ne domin ƙirƙiro abin da muka kira "sabuwar Sudan".


Sudan Wahlen Kandidat Salva Kiir
Jagoran neman mulkin kudancin Sudan Salva KiirHoto: AP

An ji wannan bayanin ne daga bakin John Garang, madugun ƙungiyar SPLA. Kuma a nan ba ya nufin 'yantacciyar kudancin Sudan, sai dai wata haɗaɗɗiyar ƙasa ta Sudan da zata haɗa arewaci da kudancin ƙasar. To sai dai kuma ba dukkan mambobin SPLA da al'umar kudancin Sudan ne suka yi masa tafi da guɗa game da wannan furuci da yayi ba, kamar yadda Alfred Lokuji, masanin tarihin ƙasar Sudan ya nunar:

Ya ce:"Garang yayi imani ne cewar zai iya rikiɗa Sudan zuwa wata sabuwar ƙasa ta Sudan, mai bin manufofin demokraɗiyya da kuma raba batutuwan addini da siyasa. Ƙasar da za a yi zaman cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da juna tsakanin 'yan Afirka da Larabawa. Wannan ra'ayi ne da ya samo tushensa daga tunani mai zurfi, amma da yawa daga 'yan kudancin Sudan na cike da fushi da ɓacin rai saboda saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiya ta 1972 da 'yan arewaci suka yi. Babban buƙatarsu shi ne cikakken ikon cin gashin kai."

Sai dai kuma duk da haka an hangi wata kyakkyawar dama ta cimma burin John Garang.

Sudan Referendum
Abin alfahari: dan kudancin Sudan da tutar kasar saHoto: picture alliance/dpa

A shekara ta 2005 'yan tawayen SPLA tare da gwamnatin arewacin Sudan sun rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya ta zaman lafiya bayan faman kai ruwa rana ta tsawon shekaru da dama. Sun cimma daidaituwa kan ba wa kudancin Sudan ikon cin kashin kanta, inda kuma ab lokaci guda suka kafa wata gwamnati ta haɗin gambiza tsakaninsu. An shirya gudanar da ƙuri'ar raba gardama game da makomar kudancin Sudan a shekara ta 2011. Amma jim kaɗan bayan haka John Garang ya baƙonci lahira. Magajinsa Salva Kiir ya dage akan ikon cin gashin kan kudancin Sudan, lamarin da aka yanke ƙuduri kansa a hukumance a cikin watan janairun da ya wuce. Kimanin kashi 98% suka goyi bayan ikon cin gashin kan kudancin Sudan a ƙuri'ar ta raba gardama, wanda ta haka aka wayi gari Afirka zata samu wata sabuwar ƙasa cikon ta 54 bayan shekaru kimanin 50.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita: Umaru Aliyu