1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mulkin Burkina Faso a hannun matashin soja

October 6, 2022

Matasa a Burkina Faso na fatan matashin soja dan shekaru 34 da ya kifar da gwamnatin mulkin soja a kasar, zai kawo wa kasar ci gaba duk da yadda duniya ke Allah wadai da juyin mulkin.

https://p.dw.com/p/4Hq4l
Matashin soja  Ibrahim Traore mai shekaru 34 da ya kifar da gwamnati a Burkina Faso
Matashin soja Ibrahim Traore mai shekaru 34 da ya kifar da gwamnati a Burkina FasoHoto: RADIO TELEVISION BURKINA FASO/REUTERS

Majalisar dokokin ta bayyana bukatar hanzarta daukar matakan ladabtarwa da ma katse hanzarin masu yin mulki da sannu a hankali ke kara yin kutse ga mulkin dimukuradiyya a kasashen Afrika ta Yamma domin zama darasi ga 'yan baya. 

Masharhanta na bayyana cewa rashin daukar tsauraran matakai a kan masu juyin mulki na kara bude kofa ne kawai ga tsagerun sojoji da ke amfani da karfin bindiga wajen kifar da gwamnatin dimukuradiyya.