1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalaman wani soja sun haifar da muhawara

Issoufou Mamane SB/AH
April 26, 2023

A Jamhuriyar Nijar cece-kuce ya taso biyo bayan kalaman sukar lamirin kasashe makwabta da wani babban hafsan sojin kasar ya yi wadanda kuma suka haifar da martani a ciki da wajen kasar.

https://p.dw.com/p/4Qaux
Jamhuriyar Nijar I Shugabat Mohamed Bazoum lokacin ziyarar sojoji
Shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar lokacin ziyarar sojojiHoto: Gazali Abdou/DW

A yayin sallar hadin kan 'yan kasa ta kowace ranar 24 ga watan Afrilu da kasar ke shiryawa ne a garin Tchintabaraden da ke jihar Tahoua, shugaban hukumar wanzar da zaman lafiya Janar Abou Tarka ya soki lamirin kasashen Burkina Faso da Mali a dangane da manufofinsu na dakatar da hulda da kasashen Yamma inda ya ce hakan zai jefa su cikin mummunan yanayi kasancewar sun mayar da kansu shanun ware a cikin dangi sabanin kasar ta Jamhuriyar Nijar da ke samun tallafi ta ko'ina daga kasashen Turawa.

Kalaman dai sun janyo martani a ciki da wajen kasar musamman a kafofin sada zumunta na zamani. Tuni dai kungiyoyin fararen hula suka yi ca ga kalaman ta hanyar mayar da martani. Masu nazarin al'amura na yau da kullum sun nuna fargaba game da yanayin da 'yan kasar ta Jamhuriyar Nijar da ke zaune a kasashen Mali da Burkina Faso ka iya fadawa sakamakon irin wannan kalaman inji Mounkaila Amadou dan jarida mai sharhi a kan al'amuran tsaro.

Ya zuwa yanzu dai kasashen na Mali da Burkina Faso ba su ce komai ba a kan kalaman yayin da gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Nijar ta yi gum da baki.