1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yunkurin kwashe sojan Faransa daga Mali zuwa Nijar

Gazali Abdou Tasawa AMA
September 20, 2021

Ministar tsaron Faransa Florence Parly ta tattauna da mahukuntan Jamhuriyar Nijar kan yunkurin maido da hedikwatar sojojin Faransa masu yaki da ta’addanci a Sahel daga Mali zuwa Nijar.

https://p.dw.com/p/40ZOa
Mali Frankreich beendet die Operation „Barkhane“
Sojojin Faransa na rundunar Barkhane da ke shirin barin MaliHoto: AP Photo/picture alliance

Ministar tsaron kasar ta Faransa Florence Parly wacce ta isa a birnin Yamai a wannan Lahadi ta soma ne da ganawa da takwaranta ministan tsaron kasar Nijar Alkassoum Indatou kafin daga bisani ta gana da shugaban kasa Mohamed Bazoum a Fadarsa, tare da tattaunawa da shi kan batun yaki da ta’addanci da kuma rawar da ya kamata Nijar ta taka a sabon tsarin zaman sojojin Faransa a Sahel bayan ficewarsu daga kasar Mali. Kuma a firar da manema labarai Florence Parly ta ce "Tana mai cike da farin ciki dangane da yadda wannan tattaunawa ta tsakanin Faransa da Nijar ke ci gaba da gudana cikin aminci da mutunta juna,kuma dubin alkibla daya. Na jaddada wa Shugaba Bazoum cewa Faransa za ta ci gaba da kawo gudunmawarta ga kasashen Sahel da ga rundunar G5 Sahel. Sannan Faransa za ta ci gaba da karfafa zaman sojojinta a Sahel musamman a Nijar."

Karin Bayani: 'Yan majalisa sun koka kan tsaro a Tillaberi

Ko da shi ke cewa Ministar kasar ta Faransa ba ta yi cikakken bayani ba kan batun karfafa huldar shawo kan matsalar tsaro da Faransar take son yi da Nijar ba, wasu rahotanni sun bayyana cewa Faransar wacce tuni ta soma aiwatar da shirinta na rage sojojinta a Sahel daga dubu biyar zuwa dubu biyu da 500 ko dubu uku, na son maido da babbar hedikwatar sojojin nata na yankin Sahel ne a kasar Nijar, inda da ma take da wata karamar hedikwatar sojoji mai kunshe da sojoji 700 da jiragen yaki guda shida da marasa matuka na Drone guda shida, wadanda a halin yanzu take son ta kara yawansu dan ci gaba da harar ‘yan ta’adda a yankin magangamar iyakoki uku na Nijar Mali da Burkina Faso inda ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi suka yi kakagida. 

Frankreich Mali - Militär Konflikte
Sojan Faransa tsaye da takwaransa na Mali Hoto: Frederic Petry/Hans Lucas/picture alliance

Karin bayani: Kafa rundunar sintiri ta Turai a yankin Sahel

Wannan yinkuri na neman karfafa huldar harkokin tsaro tsakanin Faransa da Nijar na zuwa ne a daidai loakcin da kasashen Afirka da dama irin su Mali da ma Guinea ke neman raba gari da Faransa a fannin harkokin tsaro. Kuma Malam Son Allah Dambaji shugaban kungiyar fafutikar kare hakkin dan Adam ta ROAD ya ce "Matakin ba alkahiri ba ne ga Nijar kana yana iya dusashe kwarjinin da shugaban kasar Mohamed Bazoum yake da a idon ‘yan kasar da dama tun bayan hawansa mulki."

Faransar dai ta bayyana cewa  tana jiran lamuncewar mahukuntan kasar ta Nijar kafin aiwatar da wannan shiri na maido da babbar hedikwatar sojojin Faransa na Sahel daga Mali zuwa Nijar. Sai dai har a karshen ganawarta da shugaban kasa Mohamed Bazoum Ministar tsaron kasar ta Faransa ba ta bayyana matsayar da suka cimma da shugaban ba a kan wannan batu kuma ita kanta gwamnatin ta Nijar ba ta ce komai ba a kai.