1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru hudu ana gina gadar da ke Maputo

November 13, 2018

A kasar Mozambique an kammala aikin gadar da ta ratsa kogin Maputo zuwa Katembe. Godiya ga masu zuba jari na China da kuma kamfanonin gine gine wajen tabbatar da aikin gadar da ke zama daya daga cikin mafi tsaho a duniya

https://p.dw.com/p/389cF
Mosambik - Einweihung der Maputo-Katembe-Brücke: größte Hängebrücke Afrikas
Hoto: DW/R. da Silva

 

Babu shakka gadar abar kallo ce da daukar ido. Da wasu manyan turaku biyu a gabar kogi da suka bada kariya ga gadar da kuma wasu manyan wayoyi masu launin ja da rastin rawaya daure a jikinta. Gadar mai tazarar fiye da kilomita uku ta tsallake kogin Maputo. Matafiya masu son zuwa Afirka ta kudu kan shafe tsahon sa'oi akan ruwa kafin su isa ko kuma su yi jiran tsammani na tsahon lokaci ga jiragen da basu da tabbas. Amma a yanzu duk wannan ta kau. Ga yan kasar Mozambique da dama gina gadar alheri ne kamar yadda wannan matar Lucinda da ke yin aikatau ta baiyana.

" Gina gadar dabara ce mai kyau, misali ga mutanen da ke zaune a Katembe musamman masu zuwa makaranta ko jami'a ko kuma wuraren aiki za su amfana, haka ma kuma jama'a da ke wucewa za su ji dadi na kashe kwarkwatar idanunsu."

Lucinda na zaune ne a Maputo kuma ta kan yi yawan tafiye tafiye zuwa Katembe tare da 'yayanta, a yanzu za ta sami saukin tafiyar.

Kwararrun masu zanen taswirar gine gine da Injiniyoyi a duniya sun yaba tsarin gadar da cewa abin sha'awa ne da kayatarwa. Ta dangana da mashigin tashar ruwa na kasa da kasa. Manajan gudanar da aikin Bai Pengyu na kamfanin China da ke gudanar da aikin gina tituna da gadoji ya ce babu matsala ko kadan tattare da aiki.

Mosambik - Einweihung der Maputo-Katembe-Brücke: größte Hängebrücke Afrikas
Gadar da ta fi tsawo a AfirkaHoto: DW/R. da Silva

"Abin bai shafi kofar shiga tashar jiragen ruwan ba, tsawon mita 60 ne daga kasan gadar zuwa saman ruwan wanda hakan zai yi tasiri ga cigaban birnin. Manyan jirage za su iya shigowa gabar ruwan Maputo kuma mun yi tsarin yadda za a amfana a gaba."

Haka ma dai Injiniyoyi a Nuremberg da ofishinsu ke cikin wadanda suka gudanar da aikin musamman kula da karfin kankare na turakun gadar suke gani. Kasar China ce dai ta samar da kudin gudanar da aikin. Jose ma'aikacin tsaro ne na wani kamfani a Maputo, yana ganin cewa aikin abu ne mai kyau amma ya soki lamirin makudan kudaden da aka kashe a aikin.

"Yace idan ana maganar kudi, babu shakka gadar ta ci kudi masu yawa domin ta lakume kimanin dala miliyan 900, a saboda haka mayar da wannan kudi na bukatar goyon baya, kamar yadda ka sani Bankin China shi ya tallafa."

Kamfanin da ya gudanar da aikin gina gadar ya shigo da galibin kayan ginin ne daga China. Kuma tsabar kudi fiye da euro miliyan 600 kudi mai yawa musamman idan aka yi la'akari da cewa Mozambik tana daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya. To sai dai kuma a cewar Manuel wani dan kasar ta Mozambique gadar za ta taimakawa harkar kasuwanci tsakanin Mozambique da Afirka ta kudu kuma za a sami mutane da dama 'yan yawon bude da za su ziyarci wuraren shakatawa na gabar kogi.

Mosambik - Einweihung der Maputo-Katembe-Brücke: größte Hängebrücke Afrikas
Gadar Maputo zuwa KatembeHoto: DW/R. da Silva

"Hanyar gadar ta fi sauri, ga masu yawon bude ido alal misali kana iya kaiwa wurin cikin sauki kuma ka dawo nan da nan. Za mu dauki kamar shekaru 30 zuwa 40 domin biyan kudin, ya danganta dai da harajin da aka sa na hawa gadar"

Da farko an tsara motoci da su yi tafiya a kan gadar za su biya euro daya da centi 90 ga motoci kanana yayin da manyan motoci kuma za su biya euro 17 da centi 50. Su kuwa motocin Bus Bus za su sami dan rangwame. To amma duk da haka kudin ya yi tsada, ya wuce kimar rayuwar yan Mozambik. Yawancin mutane dai na tafiya ne a kasa, to amma ba a samar da hanyar da masu keke za su bi ba a kan gadar. Wasu masu sukar lamirin gadar kuma sun yi zargin cin hanci ya shiga cikin lamarin yayin da wasu ke cewa kasar ta fi bukatar makarantu da asibitoci cikin gaggawa maimakon gina gada.