1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mota ta ji wa mutane da dama rauni a London

Mouhamadou Awal Balarabe
October 7, 2017

Mutane akalla 11 sun ji rauni a birnin London bayan da wata mota ta buge gungun mutane a kusa da babban gidan adana kayan tarihi da 'yan yawon shakatawa ke yawan ziyarta.

https://p.dw.com/p/2lRAm
UK Fahrzeug verletzt mehrere Fußgänger in London - Mann festgenommen
Hoto: Reuters/P. Nicholls

'Yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da buge mutane da mota a kusa da babban gidan adana kayan tarihi na London. Sai dai masu bincike ba su sanya abin da ya faru a matsayin harin ta'addanci ba, duk da cewa mutane 11 sun ji rauni.

Hotuna da aka watsa ta kafar Twitter sun nuna mutum sanye da riga mai launin bula da tattatsin jini a fuskarsa. Sai dai wasu mutane biyu ake kyautata zaton wadanda suka shaidar da lamarin ne sun kamashi. 'Yan sanda sun rufe wuraren da ke kusa da gidan adana kayan tarihin, yayin da jami'an agaji ke gudanar da aikin ceto.

A wannan shekarar dai birnin London ya fuskanci hare-haren ta'addanci sau biyar. Ko a tsakiyar watan Satumba sai da wani bam ya fashe a cikin jirgin karkashin kasa na London, inda kimanin mutane 30 suka ji rauni. A hare-haren da aka kai a babban birnin na Birtaniya da kuma birnin Manchester ma, an kashe mutane da yawa.