Mota mai inganci kirar Beetle-VW
Motar da masu ra’ayin gurguzu suka fara hadawa ta zamo abar sha’awa a fadin duniya: Shekaru 80 Adolf Hitler ya kafa ginshiki na samar da VW da ake kira Beetle a jihar Lower Saxony, yanzu motar na ci gaba da bunkasa.
Motocin Volkswagen na farko
Kaddamar da babban aiki: Hitler da wannan samfuri na "Volkswagen" ya kaddamar da aikin samar da Volkswagen a jihar Lower Saxony a ranar 26 ga watan Mayu na shekarar 1938. Makirkirin motar Ferdinand Porsche nan ya kafa ginshikin motar da za ta karade kasuwannin duniya.
Sauyi zuwa budaddiyar mota
Sojoji sun zama jagaba: Lokacin yakin Hitler an samar da motar ta Volkswagen budaddiya, tana da nauyi da ya kai kilogiram 950 sun zama ja gaba yadda suke kutsa kai a hanya. Janar von Manteuffel na kokarin fitar da sojansa bayan makalewa a tabo.
Mun sake dawowa
Shekaru goma kawai bayan yakin duniya na biyu, motocin na Beetle miliyan daya aka samar a kamfanin samar da motocin na Wolfsburg a ranar 5 ga watan Agusta na shekarar 1955, samfurin wannan mota da yanayin injinta ya zama alamar tattalin arzikin Jamus da ya zamo abin mamaki.
Uba da uwa da 'ya da motar Beetle
Burin Volkswagen shi ne ta samar da sararin da mutane hudu za su zauna ga ta da inganci da saukin farashi, a lokutan farko da aka fara kera motoci . A shekarar 1960 burin iyalai da dama ya cika lokacin da aka fara samar da kirar VW 1200 wacce ake bude samanta, mutane su sha iska lokacin bazara.
Daga kan hanyar kwalta zuwa gona
Ba lallai ba ne ta zamo tarakata: A kan yi amfani da motar don aiyukan gona. Godiya ga karfafan madaukan taya da motar ke da su yadda take aiki a gona a shekarun 1950 inda ake dora wa motar garmar noma.
Kera wannan samfur ya zo karshe
Karshen wa’adi: A ranar daya ga watan Yuli ne a hedikwatar VW a Wolfsburg aka kera wannan Beetle ta karshe wacce ta zamo me lamba 11,916,519. A mexiko da Brazil kuwa an ci gaba da kera irin wannan samfuri.
Daga sama har kasa abin so
Viva el Vocho! Fatan tsawon rai ga motar beetle kirar Mexiko! A Puebla an ci gaba da kera irin wannan samfurin na VW ko Beetle har sai a ranar 30 ga watan Yuli na shekarar 2003 a kamfanin "Volkswagen de Mexiko", motar da ta zamo abar sha’awa a tuka musamman ga wadanda ke bikin aure.
Sake dawowa a Brazil
Wata kasa a yanayi na shauki: A shekarar 1993 Shugaban Brazil Itamar Franco ya ba da umarni na a sake dawo da kera motar Beetle a kasarsa. A tsakanin shekarar 1959 zuwa 1986 an kera motar da a Brazil ake wa lakabin "Fusca" miliyan uku da dubu dari uku. A tsakanin 1993 zuwa 1996 an sake samar da 46,000.
Daga Volkswagen zuwa motar duniya
Haka nan a kasashe da dama na duniya da suka hadar da Afirka ta Kudu da Beljiyam da Ostireliya da Indonesiya an ci gaba da samar da motar ta Beetle. Motar ta Volkswagen mota ce ta kowa a Jamus. Kimanin samfurin motar miliyan 22 aka samar kuma aka siyar a sassan duniya. A kasashe da dama kamar a nan Masar har yanzu ana amfani da wannan mota ta Beetle.
Kallo zuwa shudi
Ga masu sha’awa da masoya motar ta Beetle: A shekarar 1998 an fitar da "Sabuwar Beetle" kalar 9C zuwa kasuwa motar na da baya da fitilu irin na beetle ta asali kamar ta Ferdinand Porsche. Sai dai yanayin motar da farashinta ya sha banban da ta asali (VW Beetle).
Tsohuwar abar so na gushewa
Sabuwar yabanya kan tsohon karfe : A gaban wani ofishi a yankin Margretshöchheim wata shukar kayan marmari ke tsiro kan tsohon karfe da ya fara tsatsa. Tsohuwar Beetle ta kama hanyar samun makoma ta koriyar yabanya.