Morsi na Masar ya yi rantsuwar kama aiki
June 30, 2012Shugaban Masar Mohammed Morsi da ke zama na farko da aka zaba karkashin Jamhuriya ta biyu ya yi rantsuwar kama aiki dazu-dazunnan a gaban kotun tsarin mulkin kasar da ke birnin Alkahira. Shi ne dai shugaban farko da aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar da ke da rajin addinin musulunci, wanda kuma ba shi da alaka da sojojin kasar.
Shugaba Morsi zai yi tattaki zuwa jami'ar birnin Alkahira domin ci gaba da gudanar da shagulgulan kama aiki, tare da gudanar da jawabi ga 'yan kasar domin bayyana manufofin gwamnatinsa. Babban kalubalen da ke gaban shugaban na Masar a halin yanzu shi ne na raba madafaun iko da majalisar mulkin sojoji, wadda Mubarak ya danka wa mulki bayan da guguwar neman sauyi ta yi awon gaba da kujerarsa ta mulki.
Tuni dai Morsi da aka zaba karkashin kungiyar 'yan uwa musulmi ya fara tattaunawa da bangarorin siyasa daban daban da nufin neman kafa gwamnatin hadaka da za ta fiskanci kalubale na tattalin arziki da kuma hadin kan kasa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh