1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Morocco ta ceto 'yan cirani sama da 800

Binta Aliyu Zurmi
July 19, 2023

Sojojin ruwan kasar Morocco sun ceto 'yan cirani mutum 845 yayin da suke yunkurin tsallaka teku zuwa kasar Spain, a cewar kafofin watsa labaran kasar.

https://p.dw.com/p/4U7zY
Migrants wait to disembark from a Spanish coast guard vessel, in the port of Arguineguin
Hoto: Borja Suarez/REUTERS

Kafar watsa labaran gwamnatin Maroko MAP, ta ce mafi akasarin wadanda aka ceto sun fito ne daga kasashen Afirka da ke kudu da Hamada Sahara.

An gano gawar mutm daya a yayin ceto bakin hauren, sannan a wannan Talatar da ta gabata kungiyar AlarmPhone da ke sanya ido kan 'yan cirani a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter cewa mutum 24 sun mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale.

Kasar Morocco da ke arewa maso yammacin Afirka, mai tazarar kilomita 150 ya zuwa tsibirin Canary na kasar Spain na zama wata barauniyar hanya da bakin haure kan bi don shiga kasashen Turai.