1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mohammed Morsi ya lashe zaɓen Masar

Zainab MohammedJune 24, 2012

Ɗan takarar jam'iyyar 'yan uwa musulmi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu, bayan jinkirta sanarwar a ɓangaren hukamar zaɓen ta Masar

https://p.dw.com/p/15KdZ
epa03240544 Egyptian presidential candidate Mohammed Morsi talks during a press conference in Cairo, Egypt, 29 May 2012. The chief of Egypt's election commission, Farouk Sultan, announced on 28 May that Mohammed Morsi, who heads the Muslim Brotherhood's Freedom and Justice Party (FJP), will face Ahmed Shafik, who was the last premier under Mubarak's rule, in the run-off vote for president. The runoff is scheduled for 16-17 June, while the winner will be announced on 21 June. EPA/KHALED ELFIQI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumar zaɓen Masar ta sanar da wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka jinkirta fitar da sakamakon, bisa dalilai na tsaro da kuma zargin tabka kura-kuran da abokan hammayan biyu suka yi.

Jagororin mulkin sojin dai sun kasance cikin fargabar ɓarkewar rikici gabannin sanar da sakamakon. Duk da cewar ana sa ran sanar da sakamakon da karfe ɗaya agogon an sake jinkirtawa har zuwa kusan Sao'i biyu kafin sanar da Mohammed Morsi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Sakamakon dai ya kasance mai ɗinbin tarihi ga Masar da ma yankin Gabas ta tsakiya baki ɗaya.

Tun bayan da aka jinkirta faɗin wannan sakamako dandalin Tahrir, ya cika da magoya bayan Jamiyyar 'yan uwa Musulmi waɗanda ke haƙiƙance cewa ɗan takararsu Mohamed Morsi ne ya yi nasara.

Magoya bayan Ahmed Shafiq a ɗaya ɓangaren kuwa, wanda ya kasance tsohon Frime Minista lokacin mulkin hamɓararren shugaba Hosni Mubarak su ma suma kafin sanar da sakamakon, sun yi zaton cewar ɗan takararsu ne zai lashe zaɓen.

Wannan sakamako dai zai kasance abun farin ciki a ɓangaren 'yan uwa musulmi, waɗanda a baya ke da rinjaye a majalisar ƙasar kafin majalisar mulkin soji ta sanar da rusa shi.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita : Zainab Mohammed Abubakar