1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mo Yan ya ci Kyautar Nobel a Fannin Rubuce-rubuce

October 11, 2012

An karrama Mo Yan, marubicin kasar China da kyautar Nobel a fannin adabi ta shekarar 2012

https://p.dw.com/p/16OaK
Hoto: Reuters

Makarantar kimiya ta kasar Sweden ta ba da sanarwar ba da lambar yabo a fannin rubuce-rubuce ga Mo Yan daga kasar China. Shi dai wannan marubuci mai shekarau 57 ya na bayanin abin da ke faruwa a kasarsa ne ta hanyar tatsuniya da rubuce-rubuce na tarihi da kuma jaridu. Mo yan na zaman daya daga cikin fitattun marubutan kasar China . A kasashen yamma ya yi tashe ne da wani littafinsa mai sumna "Black Cornfield" wanda Zhang Yimou ya sarrafa a matsayin filim. A gobe Juma'a ne kuma a birnin Oslo na kasar Norway ake dakon ba da sanarwar wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2012.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman