1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kwashe ragowar dakarun Minusma zai kasance da wuya

Abdoulaye Mamane Amadou
August 28, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kwashe ragowar dakarunta a Mali zai kasance mai matukar wahala duba da kurewar lokaci da yanayin tsaro da ke addabar Mali.

https://p.dw.com/p/4Vg0K
Mali | MINUSMA I Rundunar wanzar da zaman lafiya I Majalisar Dinkin Duniya
Mali | MINUSMA I Rundunar wanzar da zaman lafiya I Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/MAXPPP/dpa/picture alliance

Shugaban rundunar Minusma a Mali El Ghassim Wane ya tabbatar da cewa duk da yake an kusa martaba wa'adin da gwamnatin Mali ta dibar wa dakarun na ficewa daga kasar kafin karshen wannan shekara, akwai rashin tabbas ga ragowar sansanonin duba da tsaikon da aka samu bayan rufe sansanin Ber da ke Arewa maso gabashin Mali.

Karin Bayani : An kai wa dakarun MINUSMA hari a Mali

El Ghassim Wane ya kara da cewa juyin mulkin Nijar a karshen watan jiya, ya kara dagula lamurran kammala kwashe dakarun na Minusma, duba da yadda sojojin rundunar ke tsanain bukatar bi a Nijar kafin tsallakawa zuwa gabar tekun Cotonou na kasar Jamhuriyar Benin ko Lome na kasar Togo.

Karin bayani : Mali: Kawo karshen aikin rundunar MINUSMA

Gwamnatin Bamako ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya wa'adin 31 ga watan Disamaban wannan shekara da ta kwashe nata-ya-nata ta bar kasar, sai dai har yanzu sansanoni hudu ne kawai suka fice, daga cikin 10 da dakarunta na Minusma ke amfani da su a Mali.