1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta shirya magance matsalar tsaron Nijar

Ramatu Garba Baba
February 2, 2022

Ministar tsaron Faransa Florence Parly na shirin kai ziyara aiki a jamhuriyar Nijar da zummar lalubo sabbin matakan magance matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

https://p.dw.com/p/46R5Q
Bildkombo I Wahlen Niger I Mohamed Bazoum und Emmanuel Macron

Wannan wani shiri ne da kasar ta Faransa da ta yi wa Nijar din mulkin mallaka, ta bijiro da shi, da zummar taimakawa Nijar shawo kan matsalolin tsaron da suka hana zaman lafiya a kasar. Miss Parly za ta yi kokarin gabatar da wasu sabbin dabaru da Faransan ta tanadar.

A baya-bayan nan al'ummar Nijar sun yi ta gudanar da zanga-zangar adawa da rawar da Faransa ke taka wa a kasar. Ziayarar jami'ar na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Mali da ta fuskanci juyin mulki har sau biyu a cikin shekara guda ke cikin hali na tsaka mai wuya da kuma tsamin dangantakar da ta kunno kai a tsakanin mahukuntan na Mali da uwargiyarta Faransan.