1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministar kuɗin Faransa ta nuna aniyar tsayawa takarar neman shugabancin asusun IMF

May 25, 2011

Chiristine Lagarde dai na samun goyon bayan dukkan ƙasashe 27 na ƙungiyar tarayyar Turai don jagorantar IMF.

https://p.dw.com/p/11O4B
Christine Lagarde, masaniyar harkokin kuɗi da na tattalin arzikiHoto: AP

Ministar kuɗin Faransa Christine Lagarde ta ba da sanarwa a hukumance na tsayawa takarar neman shugabancin Asusun ba da lamuni na duniya IMF, don maye gurbin Dominique Strauss-Kahn wanda yayi murabus a makon da ya gabata biyo bayan zarginsa na yunƙurin yiwa wata mai shara a otel fyaɗe. A gun wani taron manema labarai da ta yi a wannan Larabar a binin Paris, Lagarde ta ce za ta tsaya takarar duk da fushin da ƙasashe masu samun bunƙasar tattalin arziki suka yi na abin da suka kira babakeren ƙasashen Turai a wannan muƙami.

"Kamar yadda kuka sani tun a wasu kwanaki na yi ta samun kiraye-kirayen goyon baya daga wasu ƙasashe. Hakan ya ƙarfafa mini guiwar yanke wannan shawara ta yin takarar."

Kafofin diplomasiya sun ce Lagarde ta samu goyon bayan ilahirin ƙasashe 27 membobin ƙungiyar tarayyar Turai ta EU da ƙasar Amirka da kuma China.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu