1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ministar harkokin wajen Jamus za ta kai ziyara Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
July 12, 2024

Annalena Baerbock ta shirya kai ziyara kasashen Senegal da Ivory Coast da ke yammacin Afirka, inda za ta tattauna da jagororin gwamnatocin kasashen a makon gobe.

https://p.dw.com/p/4iEyZ
Annalena Baerbock Hoto: epd-bild/picture alliance

Ministar harkokin wajen Jamus za ta gana da sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Jiomay Fay ne a ranar Litinin a Dakar fadar gwamnatin kasar.

A ranar Talata ne kuwa babbar jami'ar diflomasiyyar Jamus din za ta isa Abidjan na Ivory Coast, inda za ta gana da Shugaba Alassane Ouattara. Daga cikin batutuwan da ziyarar Baerbock za ta maida hankali a kai, har da abin da ya shafi makamashi da ake sabuntawa da kuma shige-da-fice.

Yayin dai da wasu kasashen yammacin Afirka suka raba gari da ECOWAS da kasashen yamma, kasashen Senegal da Ivory Coast na ci gaba da yaukaka dangantakarsu da kasashen yammacin na duniya.