1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin lalata ya sauke minista a Indiya

Yusuf Bala Nayaya
October 17, 2018

Karamin ministan harkokin wajen Indiya ya yi murabus sakamakon zargin da wasu mata 'yan jarida suka yi masa. Matan dai su goma sha biyar sun yi aiki karkashin ministan lokacin da yake tsohon aikinsa na edita.

https://p.dw.com/p/36hht
Venezuela - Ankunft Außenminister Indien M.J. Akbar auf dem 17. Summit der Blockfreien Staaten
M.J. Akbar a gaba a yayin wata ziyara a VenezuelaHoto: REUTERS

Minista Mobashar Jawed Akbar ya yi murabus daga mukamin nasa ne a wannan Laraba inda ya ce ya yi haka ne don ya tunkari shari'a da wadanda ya zarga da yin karya a kansa bisa yunkurin bata masa suna.

Akbar dai ya gabatar da kara kan 'yar jarida Priya Ramani, mace ta farko da a ranar Litinin ta zargi ministan da yunkurin lalata. Wasu matan ma dai su 20 sun ce za su ba da shaida kan badalar da ministan ya nemi yi da su.

A watan Yulin 2016 ne dai Akbar ya shiga harkokin gwamnati bayan kwashe shekaru yana aiki a matsayin editan gidan jarida a Kolkata da New Delhi. A baya-bayan nan dai wasu 'yan wasan kwaikwayo a Indiya sun rika kwarmata bayanan wasu na gaba da su a masana'antar fim wadanda ke badala da su.